India

India na fuskantar bala'in yanayin zafi da ya wuce kima

Ma'aikatar hasashen yanayin kasar India ta gargadi mutane da kaucewa fita har sai rana ta yi sanyi, gudun fuskantar hasarar rayuka.
Ma'aikatar hasashen yanayin kasar India ta gargadi mutane da kaucewa fita har sai rana ta yi sanyi, gudun fuskantar hasarar rayuka. REUTERS/Ajay Verma

Yau asabar yanayin zafi ya karu matuka a India, fiye da ko yaushe a tarihin kasar, bayanda yanayin zafin a ma’aunin Celsuis ya kai kusan digiri 50.

Talla

Lamarin dai ya jefa ‘yan kasar da dama cikin fargabar fuskantar matsanancin karancin ruwa. La’akari da cewa sai nan ranar 6 ga watan Yuni ake sa ran ruwan sama zai soma sauka.

Ma’aikatar hasashen yanayi kasar ta India tace a jihar Rajasthan, yanayin zafin ya kai digiri 49.6 a ma’aunin Celsius, yayinda kuma a sauran jihohi da dama dake yammaci, arewaci da kuma kudancin kasar, yanayin zafin ya kai matakin digiri 47 a ma’aunin na Celsuis.

A babban birnin kasar New Delhi, ma’aikatar hasashen yanayin ta gargadi mutane da kaucewa fita har sai rana ta yi sanyi, gudun fuskantar hasarar rayuka.

A jihar Maharashtra kuwa da ke dake yammacin kasar, rahotanni sun ce tuni manoma suka soma fuskantar bala’in karancin ruwa a gonaki, saboda kafewar tafkuna, koguna, da sauran wuraren da ruwa ke taruwa.

A watan Mayu daya gabata, masana hasashen yanayi suka yi gargadin cewa kashi 40 na fadin kasar India ne zai fuskanci bala'in fari a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.