Asiya

China za ta dawo da Taiwan karkashin ikonta

Wasu daga cikin jiragen ruwa na yaki a tsibirin Taiwan
Wasu daga cikin jiragen ruwa na yaki a tsibirin Taiwan REUTERS/Tyrone Siu

China ta na a shirye don sake dawo da tsibirin Taiwan a karkashin ikon ta, sanarwar da Ministan tsaron kasar China Janar Wei Fenghe ya bayar a zaman taro dake gudana a kasar Singapour.

Talla

Janar din ya bayyana cewa China na shirye don yin amfani da karfi idan ta kama don cimma wannan buri nata, a karshen ya kuma zargi Amurka da ruruta wutar rikici a yankin, tareda bayyana cewa a shekara ta 1979 ne Amurka ta yanke huldar ta da Taiwan, sai dai hakan bai hana ta sayar da makamai zuwa kasar ba.

A yan watanni da suka gabata, Shugaban China a yayinda yake ganawa da membobin gwamnatin kasar ya jaddada cewa indan ta kama China zata yi amfani da karfin soji wajen sake dawo da Taiwan karkashin ikon ta.

A shekara ta 2017 dai ne shugabannin kasashen China da Taiwan suka gana da juna a karon farko tun yakin basasa da ya raba kasashen biyu, shekaru sama da 67, Shugaban China XI Jinping da takwaransa na Taiwan Ma Ying-jeou sun gama hannu na tsawon sama da minti guda, ala’amarin da ba a zaci zai faru ba a haduwar shugabannin biyu.

Shugabannin sun yi murmushi a lokacin da suke gaisawa da juna a gaban ‘yan jaridu.

Wannan dai ne karon farko da Shugabannin bangarorin biyu suka hadu tun ballewar Taiwan daga China a 1949.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI