Isra'ila-Falasdinawa

Falasdinawa sun yi watsi da shirin Amurka na sasantasu da Isra'ila

Shugaban Yankin Falasdinu Mahmoud Abbas.
Shugaban Yankin Falasdinu Mahmoud Abbas. REUTERS/Ammar Awad

Shugaban yankin Falasdinawa Mahmoud Abbas yayi watsi da shirin Amurka na kawo karshen rikicinsu da Isra’ila.

Talla

Karo na farko kenan da a ranar asabar Amurka ta bayyana abinda ke kunshe cikin shirin zaman lafiyar.

A karkashin shirin dai za’a samar da tallafin dala biliyan ga Falasdinawa da kuma karfafa tattalin arzikinsu cikin shekaru 10.

Sai dai yayin bayyana kin amincewa da shirin, wanda Jared Kushner mashawarcin shugaban Amurka ke jagoranta, Mahmoud Abbas ya ce, kamata yayi shirin ya soma warware rikicin siyasar da ke tsakaninsu da Isra’ila, ba na tattalin arziki ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.