Falasdinawa

Larabawa za su rika baiwa Falasdinawa dala miliyan 100 duk wata

Zauren taron kungiyar kasashen Larabawa a birnin Alkahira.
Zauren taron kungiyar kasashen Larabawa a birnin Alkahira. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Kungiyar kasashen Larabawa ta tabbatar da aniyar ta na baiwa kungiyar Falasdinawa Dala miliyan 100 kowanne wata.

Talla

Ministocin kudaden kasashen kungiyar da suka gudanar da taro a Birnin Alkahira ne suka bayyana matsayin nasu kan alkawarin da suka dauka a watan Afrilu domin inganta tattalin arzikin Falasdinawan dake fuskantar karancin kudi.

Kungiyar ta kuma bayyana goyan bayan ta ga samun yancin Falasdinawan ta bangare siyasa da tattalin arziki, da kuma rage dogaro da taimako daga wasu kasashe.

Alwashin kungiyar kasashen Larabawan na tallafawa yankin Falasdinu, ya zo ne kwana guda bayan da Amurka ta gabatar da shirin da take da na sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya, tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.