Duniya

Iran bata neman yaki da Amurka

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani AFP Photos/Atta Kenare

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewar kasar sa bata bukatar gwabza yaki da Amurka, amma kuma zata kare kan ta duk wani lokacin da aka nemi afka mata.

Talla

Rouhani ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da shugaban Faransa Emmanuel Macron ta waya, inda ya jaddada matsayin kasar na cewar bata bukatar yaki da duk wata kasa.

Shugaban na Iran ya bayyana cewar kasar sa na cigaba da goyan bayan zaman lafiya a yankin tekun Fasha da ma duniya baki daya.

Sakamakon takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran, kasar tayi barazanar ficewa kacaukan daga yarjejeniyar nukiliya daga ranar 7 ga watan gobe, yayin da Faransa ke gargadin ta kan daukar matakin.

Shugaba Macron wanda ya sauka a Osaka dake kasar Japan domin halartar taron kasashen G20 ya bayyana cewar zai tattauna da shugaba Donald Trump na Amurka kan batun Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.