China-Hong Kong

China ta yi tir da hatsaniyar yankin Hong Kong

Wasu masu zanga-zanga da kutsa kai Majalisar dokokin yankin na Hong Kong tare da banna kayakin gwamnati
Wasu masu zanga-zanga da kutsa kai Majalisar dokokin yankin na Hong Kong tare da banna kayakin gwamnati REUTERS/Thomas Peter

Gwamnatin China ta yi tir da hatsaniyar da aka fuskanta a yankin Hong Kong da ya kai ga lalata kadarori baya jikkatar wasu mutane, sanadiyyar zanga-zangar kin jinin gwamnatin da ta barke, inda Chinan ta goyi bayan gudanar da bincike tare da hukunta wadanda ke da hannu a hatsanaiyar.

Talla

Cikin sanarwar da China ta fitar ta nuna matukar damuwa kan yadda ta ce yankin na matsayin tamkar babu doka da oda, ta na mai cewa ya zama wajibi a dauki matakan da suka dace don kaucewa ci gaba da fuskantar makamancin lamarin.

Yankin na Hong Kong mai kwarya-kwaryar ‘yanci dai ya fara fuskantar zazzafar zanga-zanga ne tun cikin watan jiya, bayan wani kudirin gwamnati da ya nemi fara mika masu laifi China don yi musu hukunci, sai dai lamarin ya tsanata jiya Litinin dai dai lokacin da yankin ke bikin tunawa da mika shi karkashin ikon China.

Sanarwar ta China ta ce alamu sun nuna yadda tsaron yankin ke neman fin karfin mahukuntan Hong Kong.

Dokar da ta mikawa China yankin na Hong Kong a shekarar 1997 dai, ta bukaci bai wa yankin damar gudanar da shugabancinsa karkashin tsarinsa da kuma tanadin dokarsa baya ga bayar da damar ‘yancin fadar albarkacin baki tare da cikakken ikon hukunta masu laifi a sashen shari’arsa yankin na Hong Kong har zuwa shekarar 2047.

Masu adawa da Gwamnatin yankin na Hong Kong ne dai ne suka gudanar da kazamar zanga-zanga da ta kai ga arangama tsakaninsu da jami’an tsaro, bayan da masu zanga-zangar suka yiwa harabar Majalisar dokokin kasar kawanya tare da jifar tagogin Majalisar, a bangre guda kuma Jami’an tsaro suka rika fesa musu hayaki mai yaji a ido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI