Isa ga babban shafi
India

Mutane 21 sun mutu bayan ruftawar wata katanga a India

Wasu Ma'aikan agaji yayin aikin ceto
Wasu Ma'aikan agaji yayin aikin ceto REUTERS/Stringer
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 1

Akalla mutane 21 aka tabbatar da mutuwar su a birnin Mumbai na kasar India lokacin da bangon wani gini ya fadi sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwaryar da aka tafka, wanda ya tilasta tsayawar harkokin yau da kullum a birnin.

Talla

Tanaji Kamble, mai Magana da yawun hukumar agajin gaggawa a Mumbai, ya ce baya ga wadanda suka mutu, wasu da dama sun jikkata sakamakon faduwar katangar a unguwar marasa galihu.

Hukumomin birnin sun bayyana yau Talata a matsayin ranar hutu, inda suka bukaci mutane su zauna a gidajen su domin kaucewa ambaliyar da aka samu wadda ta tilasta rufe makarantu da kuma soke tashin jirage sama da 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.