Asiya

Zanga-zangar goyan baya ga yan Sandan Hong Kong

Masu goyan bayan hukumomin Hong-Kong
Masu goyan bayan hukumomin Hong-Kong REUTERS/Edgar Su

A Hong-Kong duban jama’a ne suka fito a wata zanga-zanga nuna goyan baya zuwa yan Sanda da gwamnatin yankin .Zanga-zangar dake zuwa wata daya bayan masu boren suka yi garkuwa da Majalisar dokokin tsibirin karo na farko a tarihi.

Talla

A daye Geffen,yan Sanda sun yi nasarar gano wata maboyar bama-bamai,

Yan Sanda sun bayyana masana’antar kera bama-bamai nau’in TATP a matsayin mai tattare da hatsari, sun kuma kama wani matashi mai shekaru 27 tareda gano tilin takardu na bata sunan gwamnatin Hong-Kong.

Yan Sanda na cigaba da gudanar da bincike cikin wasu biranen Tsibirin da niyar zakulo masu goyan bayan raba gari da China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.