Matasa na ci gaba da zanga-zangar kyamar gwamnati a Hong Kong

Dandazon masu zanga-zanga a Hong Kong
Dandazon masu zanga-zanga a Hong Kong REUTERS/Edgar Su

Dubun dubatar al’ummar yankin Hng Kong galibi matasa sun ci gaba da zanga-zangar adawa da matakan gwamnatin kasar a yau Lahadi, zanga-zangar da a wannan karon aka bayyana da mafi muni duk dai da nufin bore kan yunkurin mikawa China ragamar hukunta masu laifi a yankin.

Talla

Kawo yanzu dai rahotanni sun bayyana cewa ana ci gaba da fuskantar arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro wadda ta kai ga barnata tarin kayakin gwamnati.

Tun bayan mika yankin na Hong Kong ga China a shekarar 1997 wannan ne bore mafi muni da mahukuntan bangarorin biyu suka gani a tarihi, wanda ke da nasaba da wata sabuwar dokar fara aikewa da masu laifi Beijing don fuskantar hukunci, ko da dai tuni gwamnati ta janye kudurin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.