Isa ga babban shafi
Syria-Rasha

Hare-haren Rasha da Syria sun hallaka tarin farar hula a Idlib

Tashin wasu bama-bamai da suka hallaka tarin jama'a a birnin Damascus na Syria
Tashin wasu bama-bamai da suka hallaka tarin jama'a a birnin Damascus na Syria ©BULENT KILIC / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 1

Kungiyar da ke sa ido kan rikicin kasar Syria ta ce wasu jerin hare hare da dakarun Syria da na Rasha ke kaiwa yankin Idlib sun yi sanadiyar hallaka fararen hula 20 cikin su harda yarara kanana guda 5.

Talla

Kungiyar ta ce duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da kasashen duniya suka kulla, ya zuwa yanzu dakarun Syria da na Rasha sun kashe fararen hula sama da 730 a cikin watanni 3.

Sanarwar kungiyar ta kuma bayyana cewa hare haren sun shafi tarin asibitoci a Yankunan da 'yan adawa ke rike da su.

Ko litinin din da ta gabata, sai da wani rahoto ya zargi Rasha da kaddamar da hare-hare ta sama kan wata kasuwa a yankin wanda ya hallaka farar hula 22,ko dadai tuni ma'aikatar tsaron kasar ta musanta batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.