Isa ga babban shafi

Korea ta arewa ta yi sabon gwajin makami mai linzami mafi girma

Ana dai alakanta atisayen sojin da Amurka ke gudanarwa a Korea ta kudu a matsayin abin da ya harzuka Korea ta arewan gudanar da gwajin
Ana dai alakanta atisayen sojin da Amurka ke gudanarwa a Korea ta kudu a matsayin abin da ya harzuka Korea ta arewan gudanar da gwajin STR / KCNA VIA KNS / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu | Bashir Ibrahim Idris
1 Minti

Kasar Koriya ta Arewa ta yi gwajin wasu sabbin makamai masu linzami da ke cin gajeren zango guda biyu a cikin teku, matakin da ake ganin na iya tarnaki kan shirin sake komawa teburin tattaunawa kwance damarar nukiliyar kasar da Amurka.

Talla

Ma’aikatar tsaron Koriya ta Kudu ta ce daya daga cikin makaman ba’a taba ganin irin sa ba, yayin da ya yi tafiyar kilomita 690 kafin ya fada a teku.

Wannan shi ne karo na farko da Koriyar ke gwajin makamai tun bayan ganawar da aka yi tsakanin shugaba Donald Trump da Kim Jong Un a watan jiya, wanda bai samu nasara ba.

Masu sa ido na bayyana cewar atisayen sojin da akeyi tsakanin Amurka da Koriya ta kudu na daga cikin abinda ya harzuka Koriya ta Arewa wajen gudanar gwajin makaman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.