Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Gwajin sabbin makamanmu gargadi ne ga Koriya ta Kudu - Kim

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un. AP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ce gwajin makamai masu linzami guda biyu da kasar tayi, gargadi ne ga Koriya ta Kudu kan shirin atasayen hadin gwiwa da Amurka a kusa da iyakarta.

Talla

Wannan shi ne karo na farko da Koriya ta Arewa tayi gwajin makamin tun bayan da shugaba Donald Trump da Kim Jong Un suka amince su cigaba da tattaunawa domin kwance damarar mallakar makaman nukiliyar kasar.

Manyan hafsoshin tsaron Koriya ta Kudu sun ce daya daga cikin sabbin makaman masu linzami yayi tafiyar kilomita 690, kafin fadawa teku.

A baya bayan nan Korea ta Arewa ta yi gargadin yin watsi da batun komawa tattaunawar kan shirin nata na nukiliya, muddin Amurka da makwabciyarta Korea ta Kudu, basu soke atasayen soji na hadin gwiwa da suke shirin yi a wata mai kamawa ba, batun da masu sa ido suka bayyana a matsayin abinda ya harzuka Koriya ta Arewa tayi gwajin makaman.

Sojojin Amurka kusan dubu 30 ne a Korea ta Kudu, wadanda ke gudanar da atasyen hadin giwa da na kasar lokaci zuwa lokaci, matakin da Korea ta Arewa da ke kallo a matsayin tsokana da shirin mamayeta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.