Isa ga babban shafi
Asiya

Sabuwar Zanga-zangar adawa a Hong-Kong

Yan Sandar birnin Hong-Kong
Yan Sandar birnin Hong-Kong REUTERS/Tyrone Siu
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

Hukumomin Hong-Kong sun dau matakan tsaro masu karfi don dakile duk wani tashin hankali da kan iya biyo bayan sabuwar zanga-zanga da masu bore suka kira a yau asabar.

Talla

Zanga-zangar ta yau asabar na a matsayin mayar da martani biyo bayan azabtar da kuma nuna rashin mutunci da wasu tsagerun da ake dangantawa da yan daba suka aikata saman wasu mutane masu rajin kare demokkuradiya a Hong Kong.

Ranar lahadin makon da ya gabata ne wasu tsiraru sanye da farraren tufafi dauke da sanduna suka afkawa masu adawa da manufofin gwamnatin Hong Kong.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.