Isa ga babban shafi

Hong Kong ta sanya 'yan sanda na musamman kame masu bore

Jami'an 'yan sanda na musamman da suka tarwatsa dandazon masu zanga-zanga a Hong Kong
Jami'an 'yan sanda na musamman da suka tarwatsa dandazon masu zanga-zanga a Hong Kong REUTERS/Tyrone Siu
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Jami’an ‘yan sanda na musamman a Hong Kong sun yi amfani da harsashin roba baya ga hayaki mai sanya hawaye kan masu zanga-zangar da suka bijirewa umarnin hana musu bore da gwamnati ta yi a yau Lahadi, inda rahotanni ke bayyana cewa mutane da dama sun jikkata.

Talla

Zanga-zangar wadda tafi tsananta a jiya Lahadi, matasan da ke cikin masu boren akalla 200 sun yi yunkurin sake isa Ofishin China na Liaison da ke Hong Kong amma kuma jami’an ‘yan sandan da aka sanya tsare hanyoyin zuwa Ofishin suka tare su.

Wannan ne dai mako na 7 a jere da al’ummar yankin na Hong Kong galibi matasa ke gudanar da zanga-zangar wadda ta juye zuwa ta kyamar gwamnati tun bayan fara bore da dokar fara aikewa da masu laifi don fuskantar hukunci a China.

Ko a makon jiya matasan wadanda suka rufe fuskokinsu da mayani sun rika jifan Ofishin na Liaison da kwai suna fadin bama bukatar katsalandan din China.

Masu boren dai na neman lallai a tabbatar da bin tsarin Demokradiyya a shugabancin yankin tare da neman shugabar yankin ta ajje aikinta baya ga janye duk wani yunkurin shigowar China a harkokin tafiyar da gwamnati.

Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zangar sun kai tsakiyar dare suna boren matakin da ya bayar da damar kame da dama galibi matasa mata da maza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.