Myanmar-Rohingya

Myanmar na tattaunawa da 'yan Rohingya kan komawarsu gida

Wasu 'yan kabilar Rohingya yayin zanga-zangar adawa da kisan kiyashin da ake musu a Mynamar
Wasu 'yan kabilar Rohingya yayin zanga-zangar adawa da kisan kiyashin da ake musu a Mynamar REUTERS/Mohammad Ponir Hossain

A yau Lahadi, tattaunawa ta ci gaba tsakanin mahukuntan Myanmar da jagororin ‘yan gudun hijirar kabilar Rohingya da ke Bangladesh dangane da batun komawarsu gida.

Talla

Tun a jiya Asabar ne tawagar wakilan gwamnatin Myanmar, karkashin jagorancin ministan wajen kasar U Myint Thu suka isa Bangladesh da nufin kammala kulla yarjejeniyar komawar Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da rikici ya raba da gidajensu gida.

Wakilcin na Myanmar na kokarin cimma matsaya da jagororin 'yan gudun hijirar Rohingya da ke kasar ta Bangladesh game da sharuddan da suka gindaya kafin komawarsu gida.

Yanzu haka dai akwai ‘yan Rohingya fiye da dubu 740 da rikici ya koro daga jihar Rakhine cikin shekarar 2017 wadanda ke matsayin kari kan ‘yan gudun hijira dubu dari 2 da ke zaune a sansanin Cox Bazar cikin kasar ta Bangladesh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.