Isa ga babban shafi
China-Hong Kong

Dole a hukunta masu zanga-zangar Hong Kong- China

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Hong Kong
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Hong Kong 路透社
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Gwamnatin China ta jaddada goyon bayanta ga shugabar Hong Kong da jami’an ‘yan sandan yankin, inda ta ce, dole ne a gaggauta hukunta masu zanga-zangar da suka sake fantsama kan tituna a karshen mako don ci gaba da nuna adawa da tsarin tafiyar da gwamnatin Hong Kong.

Talla

Kimanin watanni biyu kenan da al’ummar Hong Kong suka fara gudanar da zanga-zangar adawa da kudirin dokar tasa keyar masu laifi zuwa China don fuskantar hukunci, yayinda zanga-zangar ta rikide ta koma tattakin kare manufofin Dimokaradiya.

China dai ta fitar da jein sanarwar tir da zanga-zangar wadda ta yi sanadiyar rugujewar babban burin mahukuntan Beijing na mika musu masu laifi daga Hong Kong.

A halin yanzu dai, kasar ta China ta mika wa gwamnatin Hong Kong ragamar daukar matakin magance matsalar zanga-zangar.

Bayanai na cewa, masu zanga-zangar na cikin shirin ko ta kwana domin fuskantar duk wani martanin da ka iya kunno kai daga Beijing, yayinda babban jami’n China da ke kula da al’amurran da suka shafi Hong Kong, ya kira taron manema labari na musamman a wannan Litinin.

Babban jami’in na China ya shaida wa manema labaran cewa, babu wata gwamnati da za ta amince da irin wannan tarzoma, yana mai zargin wasu tsirarun masu tsattsauran ra’ayi da rura wutar rikicin Hong Kong.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.