Afghanistan

MDD ta bayyana kaduwa da adadin salwantar rayuka a Afghanistan

Kusan fararen hula dubu 1 da 400 ne suka halaka a Afghanistan cikin watanni 5 a shekarar 2019.
Kusan fararen hula dubu 1 da 400 ne suka halaka a Afghanistan cikin watanni 5 a shekarar 2019. AFP/NOORULLAH SHIRZADA

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kaduwa kan irin fararen hular dake mutuwa ko kuma jikkata a Afghanistan wadda ta kwashe shekaru 18 tana fama da tashin hankali, lamarin da tace tilas a kawo karshensa.

Talla

Alkaluman da ofishin Majalisar ya gabatar na baya bayan nan ya nuna cewar an samu raguwar mutanen dake gamuwa da tashe tashen hankulan da kahsi 30 a watanni 6 na wanna shekara, sabanin adadin da aka gani bara, amma duk da haka, rikicin ya lakume rayukan mutane 1,366, yayin da 2,446 kuma suka samu raunuka.

Duk da raguwar tashin hankalin, Majalisar ta bayyana adadin a matsayin abin takaici.

Tuni dai tattaunawa tayi nisa tsakanin Amurka da wakilan kungiyar Taliban da ke gwabza yaki a Afghanistan, son kawo karshen tashin hankalin.

Tattaunawar na gudana ne a Doha babban birnin kasar Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI