Isra'ila-Falasdinawa

Isra'ila za ta ginawa jama'arta gidaje 6000 a yankin Falasdinawa

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu REUTERS/Ronen Zvulun

Gwamnatin Isra’ila ta amince da gina sabbin gidaje har guda dubu 6 a yankin Yammacin Kogin Jordan na Palasdinu, tare da bai wa Falasdinawan damar gina gidaje 715.

Talla

Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ne ya fara tado batun gina wadannan sabbin matsugunai kafin daga bisani su samu amincewar gwamnatin kasar baki daya.

Da gagarumin rinjaye ne wannan shawara ta samu karbuwa lokacin da aka gabatar da ita gaban majalisar tsaron kasar a tsakiyar daren jiya talata.

Duk da cewa za a gina gidaje dubu 6 domin yahudawa da kuma 715 karo na farko domin Palasdinawa, to amma ga alama shirin zai fuskanci tirjiya daga mahukuntan yankin na Palesdinu da ke kallon matakin a matsayin mamaya.

Haka zalika a bangaren Yahudawan ma akwai wadanda ke adawa da gina gidaje 715 domin Palesdinawan.

Yankin da ake shirin gina wadannan gidaje a gabar yammacin kogin Jordan, a karkashin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka sanya wa hannu a birnin Oslo a shekarar 1994, zai ci gaba da kasancewa ne karkashin kulawar Isra’aila amma ba tare da yin wasu gine-gine ba a kansa.

An dai bayar da wannan izni ne a ranar da manzon musamman na shugaba Donald Trump Jared Kushner ke ziyara a birnin Jerusalem.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.