Saudiya

Masana sun yi hasashen tsananin zafi yayin aikin Hajji a Saudiya

Dakin ka'aba a garin Makka mai girma
Dakin ka'aba a garin Makka mai girma REUTERS/Ahmed Jadallah/File Photo

Masana yanayi a kasar Saudi Arabia sun yi hasashen cewa za a iya fuskantar tsananin zafi a lokacin aikin hajjin bana, wanda ka iya maki 50 a maaunin zafi na Celsius.

Talla

A cewar sashen kula da yanayi na kasar Saudi Arabia, yanayin dumin gari a wasu sassan kasar galibi Makka da Madina ka iya karuwa zuwa kashi 85, wanda zai kara tsananin zafin da za a fuskanta.

Haka zalika hasashen masanan ya nuna cewa za a iya fuskantar ruwa a garin Makka amma bayan gajimaren da zai rufe sararin samaniya na tsawon lokaci wanda shima zai kara dumin gari.

Sai dai hasashen ya bayyana cewa, duk dai a ranakun aikin hajjin za a fuskanci kakkarfar iska da ke dauke da hazo ko kuma tun daga safiya zuwa maraice musamman a garin Makka.

Ko yayin aikin hajjin 2018 ma, an ga yadda aka fuskanci ruwa a ranar farko ta fara gudanar da aikin hajji a kasar ta Saudi Arabia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.