Taliban ta bukaci dakatar da zaben Afghanistan

Wasu wakilan kungiyar Taliban
Wasu wakilan kungiyar Taliban KARIM JAAFAR / AFP

Kungiyar Taliban ta gargadi gwamnatin Afghanistan kan ta dakatar da matakin gudanar da zaben da ta ke shiryawa cikin watan Satumba mai zuwa.

Talla

Cikin sakon da ta aike ga gwamnatin kasar, Taliban ta nemi Afghanistan ta kauracewa zaben na ranar 28 ga watan Satumba, ko kuma ta kaddamar da hare-haren da za su haddasa tarnaki a kasar.

Ko a wancan lokacin da aka tsara gudanar da zaben na kasar Afghanistan, kungiyoyi ciki har da Taliban sun rika gargadi tare da kaddamar da hare-hare, wanda ya kai ga dage zaben zuwa watan Satumban a bana.

A wannan karon ma dai a akwai masu ra’ayin ganin an sake dage zaben har zuwa lokacin da za a karkare kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tare da ajje makamai tsakanin kungiyar ta Taliban da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI