Hong Kong

China da Amurka na cacar-baka kan zanga-zangar Hong Kong

Wasu daga cikin dubban masu zanga-zanga a yankin Hong Kong.
Wasu daga cikin dubban masu zanga-zanga a yankin Hong Kong. REUTERS/Thomas Peter

Musayar zafafan kalamai ta kaure tsakanin Amurka da China, dangane da zanga-zangar masu neman kafuwar tsarin mulkin dimokaradiya a Hong Kong, wadda China ke zargin cewa akwai hannun kasashen Turai wajen assasa ta.

Talla

Yayin cacar-bakan ta baya bayan nan, Amurka ta zargi kafafen yada labaran da ke goyon bayan China ta yada labaran karya masu tattare da hadari.

Amurkan ta maida martani ne kan rahoton da wata jarida ta wallafa da ya ce wani jami’in Diflomasiyar Amurka yayi tattaki zuwa birnin Hong Kong inda ya gana da shugabannin masu zanga-zangar neman tilastawa yankin komawa tsarin dimokaradiyyar kasashen Turai.

Shugabar Gwamnatin yankin na Hong Kong, Carrie Lam ta gargadi cewa, zanga-zanga rajin mulkin dimokradiya da aka kwashe watanni biyu ana gudanarwa, na haifar da gagarumar illa ga tattalin arzikin yankin, yayinda ta bayyana shirinta na cimma matsayar kawo karshen boren.

Zanga-zangar dai ta samo asali ne saboda shirin gwamnatin yankin na tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskntar hukunci, kuma har yanzu jama’a na ci gaba da boren a duk rana ta Allah tare da arangama da jami’an ‘yan sanda, abinda ya sa kasashen duniya da dama suka hana al’umominu balaguro zuwa yankin a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI