Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta sake gwajin makamai kashi na 5 cikin makwanni 2

Daya daga cikin sabbin makamai masu linzami da Korea ta Arewa ta yi gwajinsu a baya bayan nan.
Daya daga cikin sabbin makamai masu linzami da Korea ta Arewa ta yi gwajinsu a baya bayan nan. KCNA via REUTERS

Korea ta Arewa ta sake gwajin sabbin makamai masu linzami guda biyu, a matsayin gargadi ga Amurka da kuma Korea ta Kudu kan atasayen hadin gwiwar da suke shirin gudanarwa.

Talla

Ma’aikatar tsaron Korea ta Kudu, ta ce makaman masu linzami da Korea ta Kudu ta yi gwajin, masu cin gajeren zango ne, wadanda suka yi tafiyar kilo mita 400 kafin fadawa yankin tekun da ke tsakaninsu da Japan.

Wannan dai shi ne karo na 5 da Korea ta Arewa ke gwajin makamai masu linzami masu cin matsakaici da gajeren zango, cikin makwanni 2.

A baya bayan nan Korea ta Arewa ta yi gargadin yin watsi da batun komawa tattaunawar kan shirin nata na nukiliya, muddin Amurka da makwabciyarta Korea ta Kudu, basu soke atasayen soji na hadin gwiwa da suke shirin yi a wata mai kamawa ba, batun da masu sa ido suka bayyana a matsayin abinda ya harzuka Koriya ta Arewa tayi gwajin makaman.

Sojojin Amurka kusan dubu 30 ne a Korea ta Kudu, wadanda ke gudanar da atasyen hadin giwa da na kasar lokaci zuwa lokaci, matakin da Korea ta Arewa da ke kallo a matsayin tsokana da shirin mamaye ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI