Isa ga babban shafi
Yemen

Saudiya ta kaddamar da farmaki kan 'yan awaren Yemen

Wasu daga cikin mayakan 'yan awaren Yemen da suka yiwa gwamnati da kasashen duniya ke marawa baya juyin mulki.
Wasu daga cikin mayakan 'yan awaren Yemen da suka yiwa gwamnati da kasashen duniya ke marawa baya juyin mulki. NABIL HASAN / AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Rundunar dakarun hadin gwiwar da Saudiya ke jagoranta ta kaddamar da farmaki kan mayakan ‘yan awaren kasar Yemen, da a jiya asabar suka kwace iko da birnin Aden, hedikwatar gwamnatin kasar karkashin AbdRabb Mansour Hadi da kasashen duniya ke marawa baya.

Talla

Nasarar ‘yan awaren dai koma baya ce ga yakin da Saudiya ke jagoranta don murkushe yan tawayen Houthi masu rike da wasu sassan kasar ta Yemen.

Wani kwamandan mayakan ‘yan awaren ya bada tabbacin cewa sun kwace iko da ilahirin birnin na Aden na 2 mafi girma a Yemen, yayinda wata majiya ta ce fadar gwamnatin kasar kawai ya rage su murkushe.

Juyin mulkin da ‘yan awaren masu neman ballewar yankin kudancin Yemen suka yi, ya bayyana Baraka tsakanin dakarun hadin gwiwar da ke yakar ‘yan tawayen Houthi masu iko da sauran sassan kasar, la’akari da cewa ‘yan awaren na cikin rundunar da Saudiya ke jagoranta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.