Isa ga babban shafi
India

Mutane 200 sun mutu a ambaliyar ruwa a India

Garin Kerala da ambaliyar ruwan India ya shafa
Garin Kerala da ambaliyar ruwan India ya shafa REUTERS/Sivaram V
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Michael Kuduson
Minti 2

Adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a India ya haura 200, yayinda kuma ake ci gaba zabga ruwan sama kamar da bakin kwarya a yammaci da kudancin kasar.

Talla

Jami'an agaji sun kwashe sama da mutane miliyan daya da dubu 200 zuwa wasu sansanoni domin samun salama.

Daga cikin yankunan da ambaliyar ta yi kamari, har da garin Kerala mai cike da wuraren yawon budo-ido, yayinda a shekarar bara, garin ya gamu da mummunar ambaliyar da bai taba fuskanta ba cikin kusan shekaru 100, inda mutane 450 suka mutu a wancan lokaci.

A makwabciyar jihar Karnataka kuwa, mutane akalla 48 suka mutu, inda wani jami’i ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, mutane 16 sun bace, kuma har yanzu ana neman su.

An aike da masu aikin ceto da suka hada da jami’an sojin kasa da na ruwa da na sama don gudanar da aikin ceto da samar wa wadanda lamarin ya rutsa da su sauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.