China ta alakanta zanga-zangar Hong Kong da ta'addanci

Tarzomar masu zanga-zanga da jami'an tsaro a filin giragen saman Hong Kong
Tarzomar masu zanga-zanga da jami'an tsaro a filin giragen saman Hong Kong RFI

China ta yi Tur da masu zanga-zanga a Hong Kong dake adawa da zaman yankin a karkashin ta, wadanda ta kamanta su da ‘yan ta’adda, bayan da suka gurgunta filin jiragen saman yankin tsawon awanni.

Talla

A baya bayan nan ne dai gwamnatin China ta bayyana cewa zanga-zangar ta Hong Kong na tattare da alamun soma bullar ta’addanci, bayanda wata kafar yada labaran China ta fitar da bidiyon dake nuna motocin sulken kasar na tunkarar kan iyakarta da yankin na Hong Kong.

Hakan ce ta sa shugaban Amurka Donald Trump, bayyana fargabar cewa China za ta iya amfani da karfin soja wajen murkushe zanga-zangar da aka shafe makwanni 10, masu neman karin ‘yancin Hong Kong daga karkashin China suna gudanarwa.

A baya bayan nan, masu zanga-zangar sun gurgunta ayyukan filin jiragen saman yankin na Hong-Kong, abinda ya kai ga tashin hankali, da a cikinsa suka lakadawa wasu mutane biyu masu goyon bayan gwamnatin China duka, da kuma kazamar arrangama tsakaninsu da jami’an tsaro.

Zanga-zangar Hong Kong ta soma ne kan adawa da kudurin dokar mika masu laifi daga yankin zuwa China don fuskantar hukunci, daga bisani kuma ta rikide zuwa neman karin ‘yanci daga China da kuma komawa kan tsarin mulkin Dimokaradiyar kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.