Indiya

Indiya ta fusata da katsalandan din kasashen duniya kan Kashmir

Masu zanga-zanga a Kashmir kan adawa da matakin India na soke kwarya-kwaryar yancin yankin dake karkashinta ke da shi.
Masu zanga-zanga a Kashmir kan adawa da matakin India na soke kwarya-kwaryar yancin yankin dake karkashinta ke da shi. AFP / STR

Indiya tayi Allah-wadai da abinda ta bayyana da yunkurin katsalandan da kasashe ke kokarin yi kan rikicin yankin Kashmir tsakaninta da Pakistan.

Talla

Jakadan kasar ta Indiya a zauren majalisar dinkin duniya Syed Akbaruddin, ya bayyana, haka, yayin zaman da kwamitin sulhu na majalisar yayi kan yankin na Kashmir a a Juma’ar nan, karo na farko cikin shekaru 50.

A ranar ta Juma'a dai sai da aka yi arrangama tsakanin yan sanda da masu zanga-zangar adawa da matakin Indiya na soke kwarya-kwaryar yancin yankin na Kashmir dake karkashinta a farkon wannan wata, abinda yasa Pakistan rugawa zauren majalisar dinkin duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.