An samu musayar wuta a yankin Kashmir na iyakar India da Pakistan

Wasu dandazon jama'a a yankin Kashmir
Wasu dandazon jama'a a yankin Kashmir Reuters/Akhtar Soomro

Akalla mutane biyu sun mutu ciki har da jami’in dan sanda da kuma wani da ake kyautata zaton dan ta’adda ne yayin wata musayar wuta da safiyar yau Laraba a yankin Kashmir, sa’o’i kalilan bayan Donald Trump na Amurka ya sha alwashin shiga tsakani don magance rikicin da ya kunno kai tsakanin India da Pakistan.

Talla

Rikicin dai shi ne karon farko da aka fuskanta tun bayan da India ta kwace kwarya-kwaryar ‘yancin yankin na Kashmir mai rinjayen musulmi wanda kasashen biyu suka jima suna takaddama akansa.

A bangare guda Pakisatn ta fitar da sanarwar da ke nuna cewa jami’an tsaron India sun hallaka mata mutane iko akan iyakar yankunan biyu ta hanyar harbin bindiga tun daga nesa.

Sai dai makamancin labarin da wata Jaridar India ta wallafa ya nuna cewa, dan sandan India 1 ya mutu yayinda wasu fararen hula 4 kuma suka jikkata bayan da jami’an tsaron Pakistan suka bude wuta kansu akan iyakar kasashen biyu.

Kasashen biyu na India da Pakistan masu karfin makamin nukiliya rikicinsu kan yankin na Kashmir tun bayan rabuwarsu a shekarar 1947 babbar barazana ce ga tsaron nahiyar ta Asiya dai dai lokacin da a bangare guda itama China ke ikirarin mallakar wani bangare daga yankin da su ke rigima akansa.

Cikin kalaman da Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa, yankin na Kashmir kai tsaye baza a iya mika shi ga Pakistan ko kuma India ba, la’akari da cewa yanki ne da ya kunshi Mabiya addinin Islama da kuma mabiya addinin Hindu.

Sai dai Donald Trump ya sha alwashin cewa zai yi dukkanin mai yiwuwa wajen magance rikicin kasashen biyu.

Tun bayan da India ta kwace kwarya kwaryar ‘yancin yankin na Kashmir a farkon watan Agusta, rahotanni sun bayyana cewa kawo yanzu jami’an tsaronta sun kame fiyeda al’ummar yankin na Kashmir dubu 4 da suka nuna adawa da matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.