Faransa - India

Tilas mu shiga tsakanin rikicin India da Pakistan - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da takwaransa na Indiya Narendra Modi.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da takwaransa na Indiya Narendra Modi. REUTERS/Pascal Rossignol/Pool

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da fira ministan India Narendra Modi a matsayin babban bako na musamman a taron kasashen duniya 7 masu karfin tattalin arziki gungun G7 da za ta fara gobe asabar a garin Biarritz da ke kudancin Faransa.

Talla

Shugabannin biyu sun tattauna ne dangane da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da kuma rikicin Kashmir tsakanin kasar ta India da Pakistan.

Tabbas batun tattalin arziki da kuma alakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu su ne suka fi daukar hankali a lokacin wannan ganawa, musamman gaggauta kera wa India jiragen yaki samfurin Rafale da kasar ta kulla cinikinsu da Faransa,

To sai dai shugaba Emmanuel Macron ya ce batun kasuwanci bai hana shi tabo batutuwan da za su kai ga samar da zaman lafiya tsakanin India da Pakistan a lokacin ganawar da Narendra Modi ba, musamman lura da yadda aka shiga zaman tankiya bayan India ta soke kwayar-kwaryan ‘yancin cin gashin kan yankin na Kashmir.

A wannan zamani dai India ta shiga sahun kasashen da suka fi sayen makamai a duniya, yayin da kasar ta shahra a fannin kere-keren kimiya, fannoni biyu da kasashen suka jima suna tattaunawa domin cimma yarjejeniya kan yadda za su yi aiki a tare.

A game da sarrafa nukilya a fagen da ba na aikin soji ba, yau kusan shekaru 10 kenan India na tattaunawa kan yadda Faransa za ta kere mata cibiyoyin nukiliya guda 6, kuma a cewar Emmanuel Macron, akwai yiyuwar cimma matsaya kan wannan batu kafin karshen wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.