Asiya

Mutane sun mutu a Japan sanadiyar ruwan sama

Hasashen masu kula da yanayi a Japan
Hasashen masu kula da yanayi a Japan Protect Mother Earth

A kasar Japan mutun biyu aka sanar da mutuwarsu, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, inda Hukumomin kasar suka bukaci mutane sama da dubu 670 kowa ya kama gaban sa.

Talla

Masana yanayi na gargadin cewa yankin arewacin Kyushu na cikin hadarin gaske saboda ruwan sama da ake ta shatatawa.

Gwamnatin kasar ta Japan ta yi kashedi zuwa mazaunan yankida su yi tanadin abinci da ruwan sha.

Wannan dai ne karo na biyu da wasu daga cikin yankunan Japan suka fuskanci irin wannan iftila’i.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.