Isa ga babban shafi
India

Sama da mutane milyan daya zasu rasa asalin su

Wasu daga cikin yankunan Assam da aka gudanar da wannan kidaya
Wasu daga cikin yankunan Assam da aka gudanar da wannan kidaya REUTERS/Mukesh Gupta
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

Akala mutane milyan biyu ne za su rasa asalin su ko takardar dan kasa a Indiya a yankin Assam dake arewa maso gabacin kasar.Wannan na zuwa ne bayan kidayar mazaunan yankunan Assam daga jami'an gwamantin kasar ta India.

Talla

Akasarin mutanen da wannan mataki ya shafa ,an bayyana cewa musulmai ne, biyo bayan rijista na tattance jama’a.

Kidayar mutanen da aka yi  ya kai akala milyan 31 da yan kai a wannan yankin na Assam.

Yan Sanda sun karfafa matakan tsaro biyo bayan sakamako na wannan kidaya da aka yi a yankin na Assam.

Wasu daga cikin kungiyoyin kare hakokin bil Adam na danganta wannan kidaya  a matsayin abinda ya sabawa dokokin bil Adam ganin sharrudan da ake bukata kowane daga cikin mutanen yankin ya gabatar domin tabbatar da cewa dan kasar India ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.