Isa ga babban shafi
India

India ta kare shirin rijistar al'ummar Assam bayan fuskantar suka

Matakin na Narendra Modi a jihar ta Assam mai yawan mabiya addinin Islama na ci gaba da fuskantar suka daga hukumomi da kasashen duniya
Matakin na Narendra Modi a jihar ta Assam mai yawan mabiya addinin Islama na ci gaba da fuskantar suka daga hukumomi da kasashen duniya Nicholas Kamm / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Kasar India ta kare matakin da ta dauka na rajistar Yan kasa a Jihar Assam sakamakon sukar da ta fito daga kasashen duniya da kuma majalisar Dinkin Duniyar, saboda yadda aka bayyana mutane kusan miliyan biyu a matsayin wadanda ba ‘yan kasar ba.

Talla

Jam’iyyar BJP da ke mulkin Jihar Assam ta goyi bayan matakin wanda ta ce zai rarrabe 'yan kasa da baki, yayin da masu sa ido ke bayyana matakin a matsayin yunkurin mamayar mabiya addinin Hindu.

Kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi ya bukaci India da ta daina tube rigar ‘yan kasa ga jama’a, matakin da ya ce zai dada yawan mutanen da basu da kasa ta kan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.