Asiya

Ana zargin sojojin kasar Myanmar da azabtar da yan kabilar Rohingya Musulmi

Wasu 'yan kabilar Rohingya  a Mynamar
Wasu 'yan kabilar Rohingya a Mynamar © Handout via REUTERS

Jami’an kare hakkin Bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana damuwa kan yadda sojojin kasar Myanmar ke tsare mazaje manya da kanana yan kabilar Rohingya Musulmi dake Jihar Rakhine, yayin da ake zargin sojin da azabtar da su da kuma kashe wasu daga cikin su.

Talla

Jami’an sun ce ana kama wadannan mutane ne kan zargin ayyukan ta’addanci inda ake tsare su inda babu wanda zai iya zuwa wurin, kana a azabtar da su.

Jami’an da suka gudanar da binciken sun bukaci gaggauta kawo karshen irin wannan cin zarafi a Myanmar.

Hukumomin kasar na ci gaba da musanta zargin da ake yiwa sojojin ,tareda bayyana cewa suna cikin aikin su dai kamar yada dokokin kasar suka yi tanadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.