Asiya

Tsamin dangantaka tsakanin India da Pakistan

Wani yanki dake daf da kan iyaka tsakanin India da Pakistan
Wani yanki dake daf da kan iyaka tsakanin India da Pakistan REUTERS/Stringer

Pakistan ta sanar da haramtawa jirgin shugaban kasar Indiya keta sarrarin samaniyar ta.Matakin da hukumomin Pakistan suka dau na zuwa a wani lokaci da dangantaka tsakanin kasashen biyu ke ci gaba da tsami.

Talla

Ministan harakokin waje na Pakistan Shah Mehmood Qureshi ya bayyana cewa daukar wannan mataki daga hukumomin kasar sa na da nasaba da irin rawar da India ke takawa dangane da huldar ta da Pakistan.

Sai dai ta bangaren India, kakkakin gwamnatin kasar yace ko kadan haramtawa jirgin Shugaban kasar Indiya keta sarrarin samaniyar Pakistan ya yi ban hannu da dokokin diflomasiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.