Amurka-Taliban

Harin Afghanistan da Amurka ya kashe mayakan Taliban 40

Wasu 'yan uwan wadanda harin Taliban ya rutsa da su.
Wasu 'yan uwan wadanda harin Taliban ya rutsa da su. REUTERS/Stringer ATTENTION EDITORS

Rahotanni daga Afghanistan sun ce dakarun kasar da hadin gwiwar sojin Amurka sun kashe manyan shugabannin kungiyar Taliban 2 tare da mayakansu guda 38 yayin wani farmakin hadin gwiwa da suka kaddamar a yankunan Arewaci da kuma yammacin kasar.

Talla

Wani babban jami'in ma'aikatar tsaro a Kabul ya ce an kaddamar da hare-haren ne ranar asabar din da ta gabata, bayan dakatar da tattaunawar da ke neman wanzar da zaman lafiya tsakanin Taliban da gwamnatin Amurka.

Ma'aikatar tsaro ta Afghanistan ta ce cikin wadanda harin ya ritsa da su har da gwamnan Taliban da ke kula da yankin Samangan, Mawlawi Nooruddin da aka kashe a yankin Dara-e-Soof Payeen.

Sai dai tuni Taliban ta musanta batun kisan Gwamnan, ta hannun kakakinta Zbaihullah Mujahid da ke cewa Nooruddin na nan da ransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.