Isa ga babban shafi
Isra'ila

Al'ummar Isra'ila na kada kuri'a a zaben 'yan Majalisu

Masu kada kuri'a a zaben Isra'ila
Masu kada kuri'a a zaben Isra'ila REUTERS/Nir Elias
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Al'ummar Isra'ila na cigaba da kada kuri’u a zaben Yan Majalisun kasar, wanda zai bada damar tsawaita mulkin Firaminista Benjamin Netanyahu, wanda yafi kowa dadewa kan shugabancin kasar duk da zargin cin hancin da ya dabaibaye shi, ko kuma kawo karshen ikon sa.

Talla

Netanyahu na fuskantar kalubale daga tsohon Janar na soji, Benny Gantz wanda ya hana shi samun rinjayen kafa gwamnati a zaben da suka shiga na watan Afrilu, yayin da ake kallon tsohon ministan tsaro, Avidgor Lieberman a matsayin wanda zai taka rawa wajen samun wanda zai zama Firaminista.

Akalla mutane kusan miliyan 6 da rabi ake saran su kada kuri’a domin zaben Yan Majalisun 120, kuma gobe laraba ake saran bayyana cikaken sakamko, yayin da aka jibge 'yan Sanda da sauran jami’an tsaro 18,000 domin sa ido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.