Kuskuren harin Amurka a Afghanistan ya hallaka farar hula 11
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Akalla fararen hula 11 aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyyar harin jirgi marar matuki da ake kyautata zaton Jami'an tsaron Afghanistan sun nifaci kaiwa maboyar mayakan IS da ke kasar ne amma aka samu kuskure.
Gwamnan yankin Nangarhar da lamarin ya faru Shamsul Haq ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, akwai kuma karin wasu mutane 6 da aynzu haka ke karbar kulawar gaggawa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan kasar Mubarez Atal ya tabbatarwa da cewa an nifaci farmakar mayakan IS ne a harin, ko da dai akwo yanzu babu wani bayani daga Sojin Amurka da ke kasar wadanda su ake kyautata zaton sun kaddamar da farmakin.
Kuskuren harin dai na zuwa ne bayan wani harin Bom da Taliban ta kaddamar wanda ya hallaka mutane 15 ko da dai wata majiya ta bayyana cewa adadin ka iya kaiwa 30 a nan gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu