Trump ya dage harajin da ya laftawa hajojin China

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka 路透社。

A yau juma’a shugaban Donald Trump, ya sanar da dage harajin da Amurka ta lafta wa daruruwan hajojin da ake sarrafawa a kasar China, bayan share shekara daya a karkashin wannan haraji.

Talla

Sanawar ta shugaba Trump wata alama ce da ke tabbatar da cewa ana samun ci gaba dangane da tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da China domin warware sabanin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu masu karfin tattalin arziki a Duniya.

Kafin sanarwar ta yau, a can bayan Trump ya bayyana cewa shi ne ya bayar da umurnin jinkirta lafta sabon haraji kan hajojin kasar ta China sai nan da makonni biyu masu zuwa, kuma a hasashen Amurka ba domin jinkirta daukar matakin ba, to da sabon harajin zai kasance na bilyoyin daloli.

Shugaban na Amurka wanda ke zantawa da manema labarai, ya ce a yanzu dai ba ya bukatar a cimma wata yarjejeniyar kasuwanci tsakanin shi da China sai dai watakila bayan zaben shugabancin kasar da za a yi cikin shekara ta 2020.

Har ila yau Trump ya ce Amurka ba ta da niyyar kai farmakin soji kan kasar Iran, to amma zai bayar da umurnin sanya wa kasar takunkuman da ba a taba sanya wa wata kasa ta duniya irinsu ba a tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.