Pakistan

Girgizar kasa ta kashe mutane 22 a Pakistan

Girgizar kasar ta haddasa wagegen ramukan da ke da zurfin hadiye ababawan hawa
Girgizar kasar ta haddasa wagegen ramukan da ke da zurfin hadiye ababawan hawa Reuters

Akalla mutane 22 sun rasa rayukansu, yayin da 300 suka jikkata sakamakon girgizar kasa da ta afka wa yankin arewa maso gabashin Pakistan.

Talla

Mataimakin Sufetan ‘yan sandan Pakistan, Sardar Gulfaraz, ya bayyana cewa girgizar kasar ta haifar da wagegen ramukan da ke da zurfin hadiye motoci.

Ibtli’in ya tilasta wa jama’a guje-guje a biranen kasar, inda kuma motoci da dama suka tsinci kansu a tsakankanin ramukan da girgizar ta haddasa a kan manyan hanyoyi. Wasu motocin kuma sun kifa.

Alkaluman da Hukumar Binciken Ma’adinan Karkashin Kasa ta Amurka ta fitar, sun bayyana birnin Mirpur mai tazarar kilomita 20 daga Kashmir, a matsayin mafarin wannan girgizar kasar mai karfin maki 5.2.

Tuni motocin daukar marasa lafiya suka kai dauki, sannan jami’an tsaro sun hana jama’a tafiye-tafiye, tare da isar musu da agajin magunguna.

Mahukuntan kasar sun ce, girgizar ta lalata hanyoyi da turakun wutar lantarki da kuma dakunan kula da sadarwar wayoyin tarho, yayin da wasu bayanai ke cewa, gidaje sun rufta.

Rahotanni sun ce, masu aikin agaji da suka hada da sojoji na ci gaba da aikin ceto don tsirar da wadanda ke da nisan kwana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.