Isa ga babban shafi

MDD ta tsawaita wa'adi masu binciken rikicin kasar Yemen

'Yan tawayen Hutsi na Kasar Yeman a lokacin da suka taru don karban tallafin abinci.
'Yan tawayen Hutsi na Kasar Yeman a lokacin da suka taru don karban tallafin abinci. REUTERS/Khaled Abdullah
Zubin rubutu: Salissou Hamissou | Ahmed Abba
Minti 2

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar sake tsawaita wa’adin tawagar masu bincike a Yemen, wadanda suka gano shaidu kan laifukan yaki da bangarorin dake cikin rikicin suka aikata.

Talla

Bada jimawa ba, masu binciken da hukumar ta zaba a 2017, suka ce sun gano wasu mutane da suke kyautata zaton su ne ke aikata miyagun laifuka a rikicin na Yemen.

Kudirin da ya tsawaita wa’adin da shekara daya nan gaba ya hadu da adawa daga kasashe da dama, da suka hada da kasar Saudiya, dake jagorantar rundunar hadakar kasashen larabawa yan sunni, a rikicin tun 2015 domin marawa gwamnatin da kasashen duniya suka yarda da ita a gaban yan tawayen Hutsi yan shi’a dake samun goyon bayan Iran.

Manzon Saudiya a Genève, Abdulaziz Alwasil, ya zargi masu binciken da yada bayanan da ba  na gaskiya ba, da kuma ba a gudanar da sahihin bincike a kansu ba.

Daga karshe dai an kada kuri’ar amincewa da kudirin tsawaita wa’adin masu binciken na Yemen ne, bayan da Kungiyar tarayyar Turai da Canada da wasu kasashen latin Amruka suka goyi bayansa.

Jakadan Brtaniya a Majalisar Dinkin Duniya Julian Braithwaite ya bukaci masu binciken da su bi sawun goyawa bayan 'yan Hutsi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.