John Bolton ya zargi Korea ta Arewa da yunkurin karfafa Nukiliyarta

John Bolton tsohon mashawarcin shugaba Donald Trump na Amurka kan sha'anin tsaro
John Bolton tsohon mashawarcin shugaba Donald Trump na Amurka kan sha'anin tsaro REUTERS/Joshua Roberts

Tsohon mai bai wa shugaban Amurka Donald Trump shawara kan sha’anin tsaro John Bolton, ya ce har yanzu Koriya ta Arewa na da niyyar ci gaba da kera makaman nukiliyya.

Talla

Bolton wanda ke jawabi karo na farko tun bayan da aka tube shi, ya ce shugaba Kim Jong Un na Koriya na zama babbar barazana ga tsaro, saboda har yanzu ba ya da niyar dakatar da shirin kasar na nukiliya.

Koriya ta Arewan dai ita ce kasa ta farko da ta yi maraba da matakin Amurka na korar John Bolton daga bakin aiki, inda ta ce yanzu ne lokacin tattaunawa tsakaninta da Amurka za ta kankama.

Daga cikin mukarraban Trump na gaba gaba da ake ganin suna haddasa koma baya a tattaunawarsa da Koriya ta Arewan har da John Bolton wanda ko cikin watannin baya-bayan nan, sai da Koriyan ta bukaci janye shi daga tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.