Zanga-zangar Iraqi ta kazanta

Zanga-zangar adawa da gwamnati ta kazanta a birnin Bagadaza na kasar Irak.
Zanga-zangar adawa da gwamnati ta kazanta a birnin Bagadaza na kasar Irak. REUTERS/Alaa al-Marjani

Rahotanni daga Iraqi sun ce jami’an tsaro sun bude wuta kan dubban masu zanga-zangar adawa da gwamnati a birnin Bagadaza, yayinda aka shiga rana ta hudu da soma yiwa gwamnatin Fira Minista Adel Abdel Mahdi.

Talla

Akalla mutane 31 ne suka rasa rayukansu, ciki har da jami’an tsaro 2, bayan da dubban masu zanga-zangar suka yi arrangama da jami’an tsaro a Bagadaza, babban birnin kasar Iraqi jiya Alhamis, rana ta uku bayan soma bore.

Masu zanga-zangar dai sun bijirewa dokar hana zirga-zirga, hayaki mai sa hawaye da ma harbi da alburusai masu rai bai hanasu ci gaba da yin tattakin nuna adawa da gwamnatin Fira Minista Adel Abdel Mahdi ba, kan gazawa wajen magance matsalolin cin hanci da rashawa, rashin ayyukanyi da kuma ababen more rayuwa.

Kawo yanzu sama da masu zanga-zangar dubu 1000 ne suka jikkata.

Boren da Fira Minista Mahdi ke fuskanta wanda ke dada bazuwa zuwa sauran sassan kasar ta Iraqi, yafi kazanta a birnin Bagadaza da kuma Nasiriyah dake kudancin kasar, inda a nan kadai jami’an tsaro suka bindige masu zanga-zanga 7 a jiya Alhamis.

A ranar talata zanga-zangar kin jinin gwamnatin ta barke a birnin Bagadaza, inda cikin kwanaki uku ta bazu zuwa biranen kasar akalla 5, ciki har da Babylon, Basra, da Najaf.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.