Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta ce ba za ta ci gaba da ganawa da Amurka ba

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un Korean Central News Agency/Korea News Service / AP

Koriya ta Arewa ta ce ba ta da niyyar ci gaba da tattaunawa da Amurka kan makaman nukiliya har sai Amurkan ta dakatar da manufofinta na cin zarafi, kwana guda bayan rugujewar tattaunawar da suke a Sweden.

Talla

Tattaunawar ta Sweden ta zo ne bayan tsaiko na ‘yan watanni, biyo bayan ganawar da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jung Un suka yi da shugaba Trump na Amurka, kuma ta na zuwa ne bayan Pyongyang ta yi kunnnen kashi, ta gudanar da gwajin makami mai linzami a ranar Laraba.

Koriya ta Arewan dai ta fice daga tattaunawar ta Sweden, tana mai cewa ta ji takaicin yadda Amurka ta kasa gabatar mata da wata mafita mai kan – gado ba, sai dai duk da haka, Amurka na cewa a shirye take ta koma tattaunawar nan da makonni biyu.

Amma wani mai magana da yawun gwamnatin Koriya ta Arewa a ma’aikatar harkokin wajen kasar ya ce batun komawa tattaunawar da Amurka ke yi ba shi da makama, saboda haka ba ta da niyyar komawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI