Turkiya-Syria

Dakarun Turkiya sun kaddamar da hare-hare a Syria

Wani sashi na garin Ras al-Ain dake lardin Hasakeh a arewacin Syria, inda dakarun Turkiya ke barin wuta kan mayakan Kurdawa.
Wani sashi na garin Ras al-Ain dake lardin Hasakeh a arewacin Syria, inda dakarun Turkiya ke barin wuta kan mayakan Kurdawa. Delil SOULEIMAN / AFP

Dakarun Turkiya na ci gaba da barin wuta kan yankunan dake karkashin ikon mayakan Kurdawa da na IS a rewacin kasar Syria, bayan da a ranar laraba suka kaddamar gagarumin farmakin murkushe mayakan.

Talla

Jim kadan bayan soma fafatawar dakarun Turkiyan suka halaka mayakan Kurdawa 16, bayan kaiwa sananonin mayakan na Kurdawa guda 181 farmaki.

An dai shafe tsawon lokaci Turkiya na shirin kaddamar da farmakin kan mayakan Kurdawan na kungiyar YPG, masu alaka da jam’iyyar Kurdawa ta PKK da Turkiyan ta haramta, sakamakon yakin neman ballewa daga kasar da ta shiga tun daga shekarar 1984, abinda ya jawo sanya su cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Sabon farmakin dai ya tilastawa dubban fararen hula tserewa, a dai dai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya gargadin cewar, matukar dakarun Turkiya suka aikata laifukan yaki a sabon farmakin, zai tabbatar da cewa gwamnatinsa ta nakasa tattalin arzikin kasar.

Yau alhamis kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai tattauna kan halin da ake ciki, dangane da hare-haren da Turkiyan ta kaddamar a arewacin Syria.

Ita kuwa kungiyar kasashen larabawa ta Arab League ta bayyana ranar 12 ga Oktoba, a matsayin lokacin da za ta gudanar da na ta taron a Alkahira, babban birnin kasar Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.