Turkiya-Syria

Turkiya ta yi barazanar rusa yarjejeniyar tsagaita farmaki kan Kurdawa

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan. REUTERS

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan yayi gargadin dakarun kasar za su ci gaba da luguden wutar da suka dakatar kan mayakan Kurdawa a Syria, muddin Kurdawan suka ki ficewa daga cikin yankin Tudun mun tsira da Turkiyan ke son tabbatarwa nan da ranar talata.

Talla

A jiya Alhamis Turkiya da sauran kasashen kungiyar tsaro ta NATO suka amince da tsagaitar wutar farmakin da ta kaddamar kan mayakan Kurdawan a arewacin Syria, har na tsawon kwanaki 5, da sharadin Kurdawan za su janye daga yankin.

Sai dai da safiyar yau kungiyar Syrian Observatory dake sa ido kan kare hakkin dan adam a yakin kasar ta Syria, ta ce jiragen yakin Turkiya sun kai farmaki kan sansanonin mayakan Kurdawan dake kauyen Bab al-Kheir dake gabashin birnin Ras al-Ain dake kan iyakar Syrian da Turkiya, inda suka halaka fararen hula 5.

Yau Juma’a Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace shi da takwarorinsa na Jamus da Birtaniya, nan ba da dadewa ba za su gana da shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan dangane da yakin a arewacin Syria.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewa fararen hula dubu 166 suka tsere daga muhallansu tun bayan soma farmakin na Turkiya kan KUrdawan a Syria ranar 9 ga watannan, sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce adadin ya zarta dubu 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI