Lebanon

Lebanon ta gabatar da sauye-sauyen tattalin arziki

Firaministan Lebanon Saad al-Hariri.
Firaministan Lebanon Saad al-Hariri. REUTERS/Mohamed Azakir

Gwamnatin Kasar Lebanon ta gabatar da shirin sauye sauyen tattalin arziki da aka sanya a kasafin kudin shekara mai zuwa, bayan an kwashe kwanaki 5 ana gudanar da zanga zangar adawa da gwamnati.

Talla

Firaminista Saad Hariri ya ce matakan ba an dauke su bane domin domin kwantar da hankalin masu zanga zanga, sai dai domin inganta rayuwar jama’ar kasar.

Sai dai masu zanga zangar sun bayyana rashin amincewar su da sauye sauyen, inda su ke bukatar gwamnatin ta yi murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.