Isa ga babban shafi
Hong Kong

Kotu ta haramta wallafa bayanai kan 'yan sanda da iyalansu

Jami'an 'yan sandan yankin Hong Kong.
Jami'an 'yan sandan yankin Hong Kong. REUTERS/Ammar Awad
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Babbar Kotun Hong Kong ta haramta Wallafa bayanan da suka shafi rayuwar jami’an ‘yan sandan Yankin da kuma Iyalansu, ciki har da hotunansu, ta kowace kafa.

Talla

Matakin kotun, bangare ne na kokarin gwamnatin Yankin na Hong Kong wajen kawo karshen matsalar kaiwa jami’an tsaro farmaki ko cin zarafin iyalansu da masu zana-zangar neman Dimokaradiya ke yi, bayan samun cikakkun bayanai kan inda ‘yan sandan ke rayuwa da kuma iyalansu.

Hukuntin kotun ya kuma haramta duk wani matakin cin zarafi, da barazana ga jami’an tsaron yankin na Hong Kong da kuma iyalansu.

Zuwa yanzu dai gwamnatin yankin Hong Kong ta shafe akalla makwanni 20 tana fuskantar zanga-zangar adawa da ita, gami da neman komawa tsarin mulkin dimokaradiyya daga dubban mutanen yankin.

Zanga-zangar ta samo asali ne daga adawa da wani kudurin doka na mika masu laifi daga Hong Kong zuwa China don fuskantar hukunci.

A farkon makon watan Oktoba nan na 2019, shugabar yankin na Hong Kong, Carrie Lam ta kafa dokar haramtawa masu zanga-zanga fuskokinsu, matakin da ya sake fusata masu adawa da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.