Turkiya-Syria

Turkiya na tilastawa 'yan gudun hijirar Syria komawa gida - Amnesty

Wasu 'yan Syria dake gudun hijira a Turkiya.
Wasu 'yan Syria dake gudun hijira a Turkiya. REUTERS/Umit Bektas

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi gwamnatin Turkiya da yin amfani da karfi wajen tilastawa ‘yan gudun hijirar Syria dake kasar komawa yankunansu da suka tserewa.

Talla

Cikin rahoron da ta wallafa a baya bayan nan kungiyar Amnesty International ta ce wasu ‘yan gudun hijirar kasarta Syria da tatattauna da su, sun shaida mata cewar, yan sandan Turkiya sun lakadawa daruruwa daga cikinsu duka, gami da yi musu barazana, domin tilasta musu sa hannu kan takardun amincewa su koma gida Syria da suka tserewa saboda tashin hankali.

Ranar 9 ga watan nan Turkiya ta kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawa a arewacin Syria, da nufin samar da yankin tsaron da za ta maido da akalla yan gudun hijirar Syria miliyan 3 da dubu 600 da yanzu haka take kula da su.

A nata rahoton kungiyar Human Rights Watch ta ce jami’a tsaron na Turkiya suna tilastawa ‘yan gudun hijirar na Syria komawa gida ba tare basu damar karanta takardun da suka sanyawa hannu ba, kuma wasu daga cikinsu ma yankin Idlib mai tattare da hadari ake maida su.

Tuni dai Turkiya ta hannun ma’aikatar harkokin wajenta ta musanta zarge-zargen, inda ta ce tana maida yan gudun hijirar gida ne da amincewarsu.

Akalla ‘yan gudun hijirar Syria dubu 500 daga cikin miliyan 3 da dubu 600 ne ke zaune a Istanbul, babban birnin Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.