Bakonmu a Yau

Farfesa Sadik Alkafwee kan murabus din Fira Ministan kasar Lebanon Sa'ad Hariri

Sauti 03:05
Tsohon Fira Ministan Lebanon da yayi murabus Saad Hariri.
Tsohon Fira Ministan Lebanon da yayi murabus Saad Hariri. REUTERS/Mohamed Azakir

Masana sha'anin siyasa a sassan duniya na ci gaba da yin tsokaci kan matakin Fira Ministan kasar Lebanon Sa'ad Hariri na yin murabus sakamakon matsalin lambar da ya fuskanta daga dubban 'yan kasar da suka shafe makwanni 2 suna zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa.Zanga-zangar dai ta biyo bayan zargin gwamnatin ta Lebanon da gazawa wajen inganta tattalin arzikin kasar.Dangane da makomar siyasar kasar ta Lebanon, Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Farfesa Sadik Alkafwee.