IS ta nada sabon shugaba

Abu Bakr al-Baghdadi, shugaban Is da Amurkata kashe kwanan nan.
Abu Bakr al-Baghdadi, shugaban Is da Amurkata kashe kwanan nan. Islamic State Group/Al Furqan Media Network/Reuters TV

Kungiyar ISIS ta sanar da nada sabon shugaba mai suna Abi Ibrahim Al-Hachimi al-Qourahi, bayan da ta tabbatar da mutuwar jagoranta Abu Bakr al-Baghdadi.

Talla

A wani sakon murya, sabon kakakin kungiyar Abu Hamza al-Quraishi ya nuna bakin cikinsa dangane da rasuwar tsohon shugaban.

al-Baghdadi wanda ya jagoranci kungiyar tun daga shekarar 2014, kuma ya kasance wanda duniya ke nema ruwa a jallo, ya gamu da ajalinsa a hannun dakarun Amurka a farmakin da suka kai a arewa maso yammacin lardin idlib ta kasar syria.

Kungiyar ta kuma tabbatar da kashe tsohon kakakin kungiyar Abu Hassan al-Muhajjir, a wani hari na daban, wayewar garin ranar da aka kashe shugaban.

Abi Ibrahim Al-Hachimi al-Qouraishi da kungiyar ta nada a matsayin Sabon kakakin kungiyar ya yi wa Amurka kakkausar gargadi, bayan da shugaba Donald Trump ya sanar da rasuwar tsohon shugaban ta kafar talabijin.

A Sakon muryar na minti bakwai ya bayyana cewa Majalisar daular kungiyar ta yi taron gaggawa bayan da ta tabbatar da shahadar al-baghdadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI