Afghanistan

Nakiya ta halaka 'yan makaranta a Afghanistan

Hoton makamanciyar najiyar da ta halaka kananan yara 9 a Afghanistan.
Hoton makamanciyar najiyar da ta halaka kananan yara 9 a Afghanistan. Reuters

Wata nakiya da aka binne a gefen hanya ta halaka kananan yara 9 a yankin Darqad dake arewa maso gabashin Afghanistan.

Talla

Jami’an agaji sun ce baki dayan kanan yaran maza ne dalibai, wadanda shekarunsu ke tsakanin 7 zuwa 11, kuma suna kan hanyar zuwa makaranta ne a lokacin da nakiyar ta fashe.

Har zuwa lokacin wallafa labarin dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, zalika Taliban ba ta ce komai ba akai.

A watan Oktoba, majalisar dinkin duniya ta wallafa rahoton cewa an samu karuwar adadin fararen hular dake mutuwa a dalilin hare-haren mayakan IS da na Taliban da kashi 42 cikin 100, cikin har da knanan yara, bayan da a Satumba kananan yara 7 suka halaka, a dalilin tarwatsewar wata nakiya da aka binne a gefen hanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI